Dalilin da Ya Sa Ganduje Zai Gina Babban Coci a Sakatariyar APC da Ke Abuja





A yayin kai ziyarar gani da ido kan yadda aikin ke gudana, Ganduje ya fadi dalilin da ya sa yake gina coci a harabar sakatariyar jam'iyyar APC a Abuja. Duba dalilin a sashen sharhi. 


A yayin kai ziyarar gani da ido kan yadda aikin ke gudana, Ganduje ya fadi dalilin da ya sa yake gina coci a harabar sakatariyar jam'iyyar APC a Abuja. Duba dalilin a sashen sharhi. 



Dalilin da Ya Sa Ganduje Zai Gina Babban Coci a Sakatariyar APC da Ke Abuja.

 


Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam'iyyar APC na kasa ya ce ginin coci a harabar sakatariyar jam'iyyar ya kankama Ya bayyana cewa gina cocin zai kawo dai daito tsakanin mabiya addinin Muslunci da Kirista wajen gudanar da ibadojin su Ganduje ya kuma sha alwashin jawo karin yawan gwamnoni da 'yan majalisu zuwa jam'iyyar APC kafin shekarar 2024 ta kare 



Da ya ke jawabi yayin kai ziyara don ganin yadda ginin cocin ke gudana, ya ce hakan zai ba Kiristoci damar yin ibadar su a sakatariyar kamar yadda Musulmi ke yi. 




Ganduje wanda ya sha alwashin tabbatar da nasarar APC a matakan kasar ya kuma yi alkawarin bunkasa 'yan jaridar da ke aiki a sakatariyar jam'iyyar, 



Kowa ya san babu coci a cikin sakatariyar, amma yanzu mun yi sabuwa coci, saboda kawo dai daito tsakanin mabiya addinin biyu. "Mun gina shaguna a cikin sakatariyar don haramta tallace-tallace, sannan mun shirya gyara ofishin 'yan jarida ta hanyar saka sabbin kayan aiki na zamani." 

Post a Comment

0 Comments