Gaskiya ne, nayi soyayya da Nafisa, Amma yanzu kimanin shekaru uku kenan bama tare.” Inji Adam Zango.
A baya ma an sha yayata labarin cewar dantaka tayi tsami tsakanin Adam Zango da Nafisa, inda hakan ya kaisu ga shiga kotu, sai dai daga bisani, manya sun shiga maganar, inda daga karshe aka yi musu sulhu.
A wani labarin kuma, A Zango yace babban burinsa a rayuwa shine yak ware wajen magana da yaren Turanci, don haka ne ma yace yana da sha’awar komawa makaranta, don samun koda difloma ce.
A dan iskan nan mai kadawa maganganun dake ta yawo a bakunan jama’a dai yanzu shine irin so da kauna mai karfin gaske da a ke zargin ya shiga tsakanin fitattun jaruman nan na wasan Hausa fim a masana’antar Kannywood watau Adam Zango da Fati Washa.
Wannan dai na zuwa ne lokacin da hotunan jaruman biyu a tare cikin raha da daman gaske ke cigaba da bayyana a kafafen sada zumunta na zamani inda kasafai ake ganin su suna ta raha suna dariya.
Legit.ng haka zalika ta samu cewa masu sharhi akan al’amurran yau da kullum a masana’antar shiya fina-finan ta Kannywood sun lura da cewa yanzu fina-finan da jaruman biyu keyi a tare na ta kara yawa a kasuwanni.
Sai dai kuma duk da maganganun dake ta yawo a kan lamarin, har yanzu jaruman sun ki fito su tabbatar ko kuma su karyata batun wanda hakan ke kara darsa kokwanto a zukatan masu sha’awar fina-finan.
MUSTSPHA NA BURASKA DA HADIZA KABARA
Nan Da Ɗan Lokaci Kaɗan Za Ku Ji Jarumar Fina-finan Kannywood, Hadiza Kabara Ta Yi Wuff Da Ni Na Aureta, Inji Mustapha Nabraska Cikin Wata Hirarsa Da BBC Hausa
NAZIRU SARKIN WAKA DA HADIZA GABON
Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa yanzu haka akwai soyayya mai karfi a tsakanin fitattun jaruman nan na fina-finan Hausa watau Baballe Hayatu da kuma Sadiya Gyale.
Kishin-kishin din soyayyar ta su ma dai ya kara karfi ne bayan da wasu zafafan hotunan su suka fita a kafafen sadarwar zamani dauke da su cikin irin siga ta ma’aurata ko kuma ta masu shirin aure.
SHU’IBU LAWAN KUMURCI DA BALARABA MUHAMMAD







0 Comments