Yayin Da Ake Shan Daka a Najeriya, Buhari Ya Bayyana Dalilin Farin Ciki Da Ya Yi Bayan Cire Tallafi
Yayin da ake fama da tsadar man fetur a Najeriya, tsohon shugaban kasa, Buhari ya ce haka dai-dai ne Buhari ya bayyana haka ne a birnin Katsina a jiya Lahadi 31 ga watan Disamba yayin wani babban taro kan matasa Tsohon shugaban ya ce hakan ya yi masa dadi saboda yawan ziyara da mutane ke kai masa za ta ragu sosai
ya ce kara kudin mai din ya rage yawan masu kai masa ziyara tun bayan barinsa kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Buhari ya bayyana farin cikinsa kan cire tallafi da Tinubu ya yi. Hoto: Bola Tinubu, Muhammadu Buhari.
Ya kara da cewa cire tallafin mai din ya kara farashin mai din wanda ya ke tsammani zai rage baki zuwa gidansa da ke Daura. Sai dai ya ce hakan bai rage komai ba ganin yadda suka nemo wata hanyar tara kudade don kai masa ziyarar, kasar yadda DCL Hausa ya yada bidiyo


0 Comments