Dillalan Albasa 11 Ne Suka Mutu, Sama Da 50 Kuma Sun Jikkata A Wani Hadarin Mota

 




Dillalan Albasa 11 Ne Suka Mutu, Sama Da 50 Kuma Sun Jikkata A Wani Hadarin Mota



Akalla ’yan kasuwa 11 da ke kai albasa da sauran amfanin gona daga karamar hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato zuwa Jihar Neja ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani hadari.





Lamarin wanda ya afku a ranar Litinin din da ta gabata a kan hanyar Maiyama/Koko a karamar hukumar Koko-Besse ta jihar Kebbi, hadarin ya raunata wasu fasinjoji kusan 50, wadanda a halin yanzu suke samun kulawa a asibiti.


Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubabar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.




Post a Comment

0 Comments